1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya gana da 'yan Chibok

October 19, 2016

Iyayen yaran dai na son gwamnatin Najeriya ta tallafa wajen kula da lafiyar yaran haka batun iliminsu.

https://p.dw.com/p/2RRPV
Nigeria 21 Chibok-Mädchen
Hoto: Picture-Alliance/Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP

Shugaban Najeriya ya sha alwashi na ninka kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an sako kusan yara 'yan makaranta 200 da ke hannun mayakan Boko Haram fiye da shekaru biyu.

Shugaba Muhammadu Buhari a wannan rana ta Laraba ce ya gana da 'yan makarantar Chibok 21 da aka sako a makon da ya gabata. Ya kuma ce gwamnati za yi iya bakin kokarinta na ganin 'yan makarantar  sun sake sajewa da al'umma cikin kankanin lokaci.

Iyayen yaran dai na kira ga gwamnatin ta Najeriya da ta duba lafiyar 'yan matan da suka kwashe tsawon lokaci a hannun mayakan na Boko Haram.Yakubu Nkeki Shi ke magana da yawun iyayensu:

"Muna kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki nauyi na kula da lafiyar 'yan matan na Chibok da suka kubuta, bayan kula da lafiyarsu a kula da iliminsu, ilimin da mayakan suka haramta musu sama da shekaru biyu."