1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya yi kiran kai zuciya nesa

October 26, 2020

Shugaban Najeriya ya ce yana goyon bayan a gudanar da bincike domin yi wa wadanda aka kashe lokacin zanga-zangar lumana adalci, ciki kuwa har da jami'an tsaron kasar.

https://p.dw.com/p/3kQtc
Muhammadu Buhari
Hoto: DW/I. U. Jaalo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ja hankali ga bukatar kowa ya rungumi zaman lafiya, daidai lokacin da hukumomi ke fadi tashin dakatar da kwasar ganima da 'yan Najeriyar ke yi daga wuraren adana abinci a fadin kasar.

Wannan dai wani sabon babi ne da Najeriyar ke fama da shi, daga cikin rikice-rikicen da suka dabaibaye kasar a wannan lokaci.

Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriyar, na cewa Shugaba Buhari ya goyi bayan kwamitin bincike da gwamnatin jihar Legas ta kafa, domin yi wa wadanda aka kashe daga cikin masu zanga-zangar lumana da jami'an tsaro adalci.

Hakan nan ma daga cikin wadanda kwamitin zai yi bincike a kai, su ne bangarorin da bata-gari suka yi wa ta'adi lokacin zanga-zangar da ta rikide ta koma tarzoma.

Shugaba Buhari ya kuma yi kiran 'yan Najeriya da su girmama juna, yayin da gwamnati ke aikinta kan lamarin.