Chile ta yi watsi da sakamakon zaben Venezuela
August 7, 2024Shugaba Gabriel Boric na kasar Chile ya bayyana cewa kasarsa ba ta amince da Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar a karshen watan jiya na Yuli ba. Haka ya nuna shugaban na Chile mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai ya bi sahun kasashen Guatemala, da Ajentina da Peru gami da wasu kasashen na Latin Amirka bisa watsi da sakamakon zaben na Venezuela yayin da kasashen Brazil and Mexiko da ke da tasiri a yankin suka dauki matakin shiga tsakanin domin magance rikicin siyasar kasar ta Venezuela.
Karin Bayani: Shakku kan sahihancin sakamakon zaben Venezuela
Shugaba Boric na Chile ya bukaci ganin kungiyoyin kasashen duniya sun tantance kuri'un da aka kada, sai dai bai fito fili ya goyi bayan Edmundo Gonzalez wanda ke zama dan takarar bangaren adawa a zaben na kasar ta Venezuela.
A wani labarin jagoran 'yan adawan na Venezuela, Edmundo Gonzalez ya yi watsi da amsa gayyar da kotun kolin kasar ta yi masa a wannan Laraba kan zargin aikata manyan laifuka da babban mai gabatar da kara na kasar ya shigar, abin da ka iya zama saba umurnin kotu.