Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya rasu
May 20, 2024Mataimakin shugaban kasar Mansouri shi ne ya tabbatar da mutuwar shugaban kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X. Kazalika dukkan mutane biyar din da ke tare da shugaban sun mutu ciki har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian da gwamnan lardin Azerbaijan na gabashin Iran da kuma wasu jami'ai da ke kare lafiyarsu.
Karin bayani: Batan dabon jirgin da ke dauke da shugaban Iran na firgita al'ummar kasar
Raisi shi ne shugaban kasar Iran na biyu da ya mutu a kan karagar mulki, baya ga shugabaMohammad Ali Rajai da ya mutu a 1981 sakamakon tashin wata nakiya bayan juyin juya halin Iran.
Karin bayani: An kama wadanda ake zargi da hare-hare a kasar Iran
Kasashen duniya na ci gaba da nuna alhini kan mutuwar shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi wanda ake hasashen shi ne ke kan layi na zama jagoran addinin kasar wato magajin Ayatollah Ali Khamenei.
Tuni dai kungiyar Hamas ta fitar da sanarwar ta'aziyya tare da jaddada goyon baya ga jagoran addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei da gwamnati har ma da daukacin al'ummar Iran a wannan lokaci na bakin ciki a fadin kasar.
Karin bayani: Duniya ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin Israila da Iran
Kazalika shugaban mayakan Houth masu gwagwarmaya da makamai Mohammed Ali AL-Houthi, ya wallafa sakon ta'aziyya a shafinsa na X, inda ya ce marigayin ya nuna dattako wajen goyon bayan Falasdinawa tare da zama barazana ga Isra'ila.
Firaiministan Indiya Narendra Modi, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya kadu mataka kan mutuwar Dr. Seyed Ebrahim Raisi, wanda ya bada gudummuwar da ba za a taba mantawa a tarihi ba, kan yaukaka dangantakar Indiya da Iran. Haka lamarin yake a Iraqi inda ma'aikatar harkokin wajen Bagadaza ta aike da sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Iran.