An kama wadanda ake zargi da hare-hare a kasar Iran
January 6, 2024Hare-haren da kungiyar IS ta dauki alhakin kai su, sun rutsa ne da gomman mutanen a lokacin da ake tunawa da kisan jagoran mayakan juyin juya halin kasar Janar Qassem Soleimani, wanda Amurka ta halaka a ranar 3 ga watan Janairun 2020.
Mataimakin ministan cikin gida a Iran, Majid Mirahmadi ya ce ana tsare da wasu mutum biyar wadanda aka kama daga lardunan kasar dabam-dabam.
An kuma gudanar da jana'izar wadanda suka mutu a hare-haren a masallacin Amam Ali da ke Kerman, wanda ya samu halartar Shugaba Ebrahim Raisi.
Jagoran rundunar mayakan juyin juya halin kasar na yanzu, Hossein Salami ya karyata batun cewa kungiyar IS ce ta kai hare-haren tare da nuna cewa babu wani abin da ya saura na kungiyar, in banda wadanda Amurka da Isra'ila ke amfani da su a matsayin sojojin haya.