Shugaba Yoon Suk na Koriya ta Kudu na ziyara a a Burtaniya
November 20, 2023A Litinin din nan shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ke fara wata ziyarar aiki ta kwanaki 4 a Burtaniya, da nufin karfafa alaka ta tsaro da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu, don samun damar tunkarar barazanar tsaron da makwabciyarta Koriya ta Arewa ke mata, da ma sauran makotanta.
Karin bayani:Koriya ta Kudu na baje kolin makamanta
A wata ganawa da jaridar The Telegraph, Mr Yoon ya ce dalilai da dama ne suka sanya shi kai ziyarar don neman tallafi, wadanda suka hada da batun yakin Gaza da na Ukraine, da kuma yadda alaka tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa ke kara yaukaka, har ma da batun barazanar makwabciyarta China.
Karin bayani:Koriya ta Arewa za ta cigaba da kera nukiliya
Mr Yoon zai ziyarci fadar Buckingham don ganawa da Sarki Charles na Burtaniya, sannan kuma ya tattauna da firaminista Rishi Sunak daga bisani.