1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan aukuwar rikici a jihar Fiilato

Abdullahi Maidawa Kurgwi
July 20, 2018

Shugabannin al'ummomi jihar Filato tare da masana sun dukufa wajen samo matakan magance tashe-tashen hankula da ke aukuwa a wasu sassan jihar,

https://p.dw.com/p/31qRC
Nigeria Angriff von Nomaden im Bundesstaat Plateau | Muhammadu Buhari, Präsident
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

Wannan dai shi ne al’amari mafi muni da ya janyo hankulan duniya kan jihar Filato, don haka shugabanin al’ummomin jihar tare da masana suka yi ganawa tsakanin juna da zummar lalubo hanyar magance sake aukuwar irin wannan tashin hankali.

Shugaban dandalin kabilun jihar Filato PIDAN, Nanle Gujor, ya ce abin takaicci ne yadda rikicin manoma da makiyaya ya dauki sabon salo, inda ya kai ga matasa ke tsare hanyoyi suna kisan matafiya, kana wasu suka yi amfani da zanga-zangar lumana suka shiga gidan gwamnatin Filato suka yi barna.  Don haka ya zama wajibi a matsayin  shugabanin Kabiulun jihar, su yi gaggawar jan hankulan iyaye kan wannan lamari.  

Shugabanin sun koka kan yadda wasu 'yan siyasa ke fakewa da rikicin wajen jefa jihar Filato cikin mummunan yanayi, inda a kwanan baya wasu matasa suka kai wa tawagar gwamnan Filato hari tare da fasa motoci, lokacin da ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira da ke Anguldi.

Taron shugabanin ya yi Allah wadai da kashe-kashen baya-bayan nan da ya auku a wasu sassan jihar, bayan samun zaman lafiya fiye da shekaru uku ba tare da wani tashin hankali ba. 

Madam Magdalene Agwom babbar malama ce a makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Filato, ta ce a duk lokacin da aka sami barkewar rikici iyaye mata su ne ke shiga cikin bala’i. Ta ce suna fatan ci gaba da tautaunawa da zummar dakile aukuwar irin wannan tashin hankalin a nan gaba.