Shugabar Jamus dana Sin sunyi kira da gaggauta daukar mataki kan Iran
March 20, 2007Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firamiyan kasar China Wen Jiabao sun amince game da bukatar gaggauta amincewa da kudurin Majalisar Dinkin Duniya kann shirin nukiliya na Iran.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Jamus tace akwai bukatar yin hakan saboda rashin bada hadin kai daga bangaren Iran.
Kudurin wanda aka mikawa komitin sulhu na Majalaisar a makon daya gabata wanda kuma ya samu amincewar manyan kasashen duniya zai haramta dukkanin cinikin makamai da Iran tare da dakatar da kadarorin wasu jamiai da kanfanoni na kasar za Iran.
Sai dai kuma kasar Afrika ta kudu wadda ke shugabancin komitin sulhun tayi kira da a soke wasu manyan batutuwa cikin kudirin tana mai kira da kara maida hankali kann hanyar diplomasiya wajen magance wannan rikici.