Jam'iyyar APC ta rufe sayar da fom
May 10, 2022Kama daga gwamnoni na jihohi ya zuwa gwamnoni na bankuna ciki dama wajen kasar, ko baya ga ministoci, fitar da Naira miliyan dari ba wahala a cikin neman takara ta mulkin tarrayar Najeriya a shekarar badi. Daya bayan daya, masu bukata ta takarar suka rika tatse guna da manta a kokari na kai wa ya zuwa ga bukatar mulkin da ke zaman mafi tasiri a cikin jeri na sana'o'in tarrayar Najeriya a halin yanzu.
Karin Bayani: Jonathan na duba yiwuwar tsayawa takarar shugaban kasa
Kuma ya zuwa kulle cinikin neman izini na takarar da yammacin wannan Talata APC mai mulki ta kafa tarihin tara kudi mafi yawa a shekaru sittin da doriya na tarihin zabe a kasar. Sama da Naira miliyan dubu ashirin, ke cikin aljihun masu tsintsiyar a wani abun da ke daukar hankali cikin kasar da ke fatan kare siyasa ta kudi.
Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta Najeriya cikin rudani
A cikin halin kunci ne dai wasu a ciki na masu takarar suka kai ga rabuwa da kudaden da masu tsintsiyar ke fatan na iya kai ta ga nasara. Wani sabon tsarin kaucewa kisan kudi na gwamnati ne ya kai jam'iyyar APC sauyin taku da komawa ya zuwa cikin gida da nufin tara kudaden da take fata na iya kai ta zuwa ga ci gaba cikin mulki na kasar.
Duk da cewa, dokar zabe ta kasar ta kayyade yawan kudade na batarwa ga kowane mukami na takara, babu yawa na kudaden da jam'iyyun ke shirin kashewa da nufin kai wa ya zuwa ga biya na bukatunsu. Abin da ke shirin maida jam'iyyar APC irin ta tajiran da babu kamarsu a fagen siyasa kasar ya zuwa yanzu.
Barrister Isma'il Ahmed ya biya Naira miliyan ashirin da kuma ya ce , ya yi masa zafi a kokarin zama dan majalisar dattawa na kasar.
''Gaskiya da zafi musamman ni a matsayi na na shugaba a jam'iyyar APC wanda nake ganin ya kamata ace duk wanda ya yi mata hidima irin tamu to ya kamata a ba su fom kyauta ko a yi musu ragi, amma dokar jam'iyyar ke nan mun kuma biya saboda muna son mu wakilci jama'ar mu''
To sai dai kuma yawan kudin na neman sauyin taku na siyasar da kila ma wucewa da sanin miliyoyin talakawa da ke da burin jagoranci cikin kasar cikin halin babu. Malam Bashir Ahmed ya kashe Naira miliyan goma bisa bukata ta zama dan majalisa ta wakilai kuma a fadarsa mafi yawa na masu kashe darin a jam'iyyar APC, na da goyon bayan talakawan da ke tururuwar saya musu fom domin jagorantarsu. Karin Bayani: Osinbajo na neman ya gaji Buhari
Sannu a hankali, tana kara fitowa fili cewar, mafi yawa na masu ikirarin cin moriyar farin jinin talakawan na da alamun karin gishiri cikin kalamansu.