Sauyin sheka na 'yan siyasa a Najeriya
February 17, 2022Da zarar an shiga kakar zabe a Najeriya a kan ga ‘yan siyasa na ta zarya wajen chanza sheka musamman zuwa jam'iyyar da ke mulki a kasar bisa dalilai mabambanta, daya daga ciki shi ne kokari na samun kariya daga zargin da suke fuskanta na cin hanci da rashawa, inda wasu aka kai ga gurfanar da su gaban kotu. Sukan yi wannan da nufin a kawar da kai daga tuhumar da suke fuskanta sanin yanayi na rufa-rufa a gwamnati.
Matsalar cin hanci da rashawa dai babba ce a tarayyar Najeriyar musamman a tsakanin ‘yan siyasa da ma ‘yan book da ke rike da amanara da aka basu ta dukiyar kasa, abinda ya sanya kungiyoyi da dama sa ido a kai.
Kama daga gwamnoni zuwa sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da ma ‘yan siyasar da basu rike da mukami, ana ganin karuwar masu sauya sheka a Najeriyar, na baya-baya nan shi ne Sanata Emmanuel Bwacha wanda ya bar PDP zuwa APC abinda wasu ke nuna yar yatsa bisa dalilai na neman kariya ne.
Da alamun dai ba'a kamala ganin masu sauya sheka ba a kakar siyasar da aka shiga yanzu a Najeriya sanin yadda jamiyyun ke bullo da dubaru na kame madafan iko a kasar.