Muna shirye don tattaunawa da kungiyar ECOWAS -Sojojin Nijar
August 13, 2023Majalisar sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun bayyana shirinsu na hawa kan duk teburin tattaunawa da ECOWAS domin warware dambarwar siyasar kasar da ta barke tun bayan karbe mulki da tsinin bundiga a ranar 26 ga watan Agusta.
Sojojin sun bayyan haka ne a yayin ganawar da suak yi da wata tawagar jagororin addinai daga makwabciyar kasar Najeriya a birnin Niamey, wanda suka ce sun yi hakan ne da zummar buda wata kafa ta samun sauki ga kallon mai bisa ruuwa da bangaren sojan ke yi wa juna da kungiyar ECOWAS bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Wannan na zuwa ne a yayin da taron 'yan majalisun dokokin kungiyar ECOWAS ya yi fatali da gagarumin rinjaye da amfani da karfin bindiga wajen mayar da dimukradiyya a Nijar a yayin wani taronsu na ranar Asabar, inda suka bukaci kungiyar ta aika wata tawagar da za ta gana da sojojin.