1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji: Bamu san inda 'yan matan Chibok suke ba

Ubale MusaMarch 18, 2015

Rundunar tsaron Najeriyar ta ce, ba ta da masaniya kan inda 'yan makarantan na Chibok suke, watanni da dama bayan Boko Haram ta sace su a makarantarsu ta kwana.

https://p.dw.com/p/1EscA
Nigeria Boko Haram
Hoto: picture alliance/AP Photo

Sannu a hankali dai iskar tana kara kadawa, sannu a hankali kuma zahiri na gaskiya yana baiyana game da makomar 'yan mata 'yan makaranta na Chibok kusan 300 da suka share kwanaki kusan dari uku hannun kungiyar Boko Haram mai fafutuka a yankin arewa maso gabas.

A baya dai gwamnatin kasar ta Najeriya ta ce ta san inda 'yan matan suke. Sai dai tana takawa sannu da nufin kaucewar ta'adin da ke iya jawo mata bacin suna ciki dama wajen kasar, kafin sabon matsayin da a cikinsa shugaban rundunar sojan kasa ta kasar ya ce, a zahiri ba su da labarin halin da 'yan matan ke ciki zuwa yanzun nan.

Boko Haram will Mädchen freilassen
Wata yarinya da ta tsereHoto: AFP/Getty Images/P. Utomi Ekpei

Duk da cewar dai sojan sun yi nisa a kokari na kauda tasirin Boko Haram da ta koma da kananan hukumomi uku maimakon jihohi kusan ukun da take iko can baya, har ya zuwa yanzu a cewar Janar Kenneth Minimah ba wani labari game da makomar 'yan matan da suka dauki hankali ciki dama wajen kasar.

“ Ba wani labari ya zuwa yanzu. A duk wuraren da muka 'yanto, mun yi bincike, amma a zahiri na gaskiya shi ne in 'yan ta'addar suna gudu suna tserewa ne da iyalansu. Kuma wadanda muka samu basu yi mana wani bayanan da ke nuna ko an tsere da 'yan matan na Chibok ba. Sai dai da yake yakin na kara nuna alamar karewa sannan kuma yankuna na kubcewa hannunsu, zamu samu kari na bayanai”

Nigeria Protest
Gangamin bukatar ceto 'yan ChibokHoto: picture-alliance/AP Photo

Tun a farkon fari dai dama shugaban kungiyar Abubakar Shekau, ya aiyanna cefanar da yaran na Chibok da a cewarsa sun yi nisa a cikin bauta, kafin sojan su karyata tare da jadadda aniyar ceto yaran komai runtsi.

Tuni dai dama ake yi wa yankin Sahel da ke da fadin gaske kuma mai tarin rikici a cikinsa kallo na matattarar ciniki na mutane da makamai ya zuwa yanzu.

To sai dai kuma kare yakin ba tare da duriyar 'yan matan ba na iya jawo bakin jini ga gwamnatin da ke fatan tsallen murnar kame ragowar kananan hukumomi ukun da ke hannun kungiyar dama kila siyasa da batun a zabukan dake tafe.