Sojojin Najeriya na yaki da masu fasa bututun mai
October 31, 2016"Operation a watse" na fatattakar tsagerun da ke faman fasa bubututun man fetur a tsakanin jihohin Legas da Ogun ya kai wani samame da nufin cafke wadanda ke hana ruwa gudu ga fannin tattalin arzikin kasar Najeriya bisa jagorancin Rear Admiral Fergusan Boboi. A yayin wannan artabu sojojin Najeriya sun kwace jarkoki sama da dubu 60 wadanda ake dibar man fetur din zuwa kasuwannin bayan fage.
Farmakin ya hallaka wasu daga cikin tsagerun masu fasa bututun mai yayin da wasu kuma suka ranta a na kare. Shugaban tawagar sojin Rear Admiral Boboi ya ce rundunar ba za ta sassauta ba har sai ta kawo karshen fasa bututan mai a yankin, ya ce fasa bututun man dai babban zagon kasa ne ga tattalin arzikin Najeriya.
Nasarar fatattakar tsagerun ta samu ne tare da tallafin gwamnatin Jihar Legas inda babban daraktan agajin gaggawa Mr Adeniyi Tiamiyu ya ce yanzu yankunan basu da matsalar tsagerun.
Ya ce: "Burin mu shi ne mu ga cewa tsagerun basu sake dawowa ba."