Sojojin Najeriya sun jikkata Shekau
August 23, 2016Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa hari da mayakan ta na sama suka kai a sansanin Boko Haram ya hallaka wasu jiga-jigan kungiyar, inda suka yi nasarar naskasa Abubakar Shekau da ke cikin masu ikirarin shugabantar kungiyar.
Sanarwa da kakakin rundunar Sojojin Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya fitar a ranar Litinin, na cewa sun kaddamar da hare-hare ne a ranar Juma'ar da ta gabata a kauyen Taye dake yankin Gombale, inda aka jikkata wasu manyan kwamandojin kungiyar.
Sanarwar ta kuma bayyana sunayen Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman a cikin sanarwar, wan da ke nuna cewa mutanen na cikin manyan kwamandojin Kungiyar da aka hallaka a hari. Amma kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin Sojojin, kazalika su ma kungiyar ba su ce komai kan sanarwar sojojin ba.
A baya dai Sojojin sun sha ikirarin cewa sun hallaka shugaba Kungiyar Abubakar Shekau sai dai Kungiyar kan musanta ta hanyar wallafa faifen bidiyo da shugaban ke raddi.