Sojojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100
July 4, 2024Sojojin Nijar sun tabbatar da kisan 'yan ta'adda fiye da 100 a samamen da suka kai ta sama da kasa kan mabuyar 'yan ta'adda a yankunan da ke iya dar kasar da Burkina Faso.
Karin bayani :Nijar: Bukatar sakar wa 'yan siyasa mara
Rundunar tsaron Nijar ta ce ta kashe mayakan ne a matsayin martani kan mummunan harin ta'addanci da masu da'awar jihadi suka kai a makon da ya gabata tare da kisan sojoji 20 a yankin Tassia na yammacin kasar.
A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce ta kuma halaka wasu karin 'yan ta'adda takwas tare da kama wasu 19 a samamen da takai kan kasuwannin yankunan Dougouro da Bankilaré da ke iyaka da Burkina Faso.
Karin bayani : Harin ta'addanci a kasar Mali ya hallaka mutane 40
Kungiyoyin masu ikrarin jihadi dai na ci gaba da cin karensu ba babbaka a yankunan Tillaberi na yammacin Nijar mai iyaka da kasashen Mali da Burkia Faso tare da halaka dumbin fararen hula.