1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojojin sun bude wasu iyakoki

Salissou Boukari LMJ
August 2, 2023

Batun bude kan iyakoki tsakanin Nijar da wasu kasashe makwabtanta ya janyo cece-kuce musamman daga yankunan da ba a sanar da bude kan iyakokin ba, inda ake da tarin motoci suna jiran ficewa zuwa kasashensu daga kasar.

https://p.dw.com/p/4UhcG
Nijar | Mohamed Bazoum | Juyin Mulki | Sojoji | Abdourahamane Tchiani
Jagoran juyin mulkin soja a Nijar Abdourahamane TchianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Daga cikin iyakokin da sojojin na Nijar suka sanar da bude wa bayanrufe su da suka yi sakamakon juyin mulkin da ya gudana a kasar kamar yadda mai magana da yawunsu Kanal Amadou Abdourahamane ya sanar, sun hadar da iyakokin sama da kasa na tsakanin Nijar da Algeriya da Libiya da Chadi da Mali da Burkina Faso. Tuni dai masu lura da al'amura kamar shugaban kungiyar Muryar Talaka na kasa a Nijar din Nassirou Seidou ke da ra'ayin cewa, lalle iyakokin da aka bude ci-gaba ne sosai amma kuma iyakar Benin da Najeriya na daga cikin na sahun gaba da jama'a ke jiran su ji cewa an bude saboda zirga-zirga mai yawa da ake yi a tsakaninsu da Nijar din.

Nijar | Mohamed Bazoum | Juyin Mulki | Sojoji | Abdourahamane Tchiani | Najeriya | Iyaka
Kan iyakar Najeriya da Nijar, na daga cikin wadanda ake fatan sake bude suHoto: DW/Y. Ibrahim

A halin yanzu dai direbobi da dama masu daukar motoci na tuwaris na can a kasar Benin suna jiran a saki hanya domin su fice zuwa kasashen Nijar da Najeriya da ma sauran kasashe na yammacin Afirka, kuma a cewar Boubakar Air Gaya ya kyautu a samu sulhu tsakanin magabata, ko lamura sa daidaita a kan iyakokin da aka rufe. Shi dai wannan lamari na rufe kan iyakoki a halin yanzu, ka iya kasancewa umarni daga bangarori dabam-dabam. Idan har wa'adin da ECOWAS ta bayar ya cika ba tare da samun wani cikakken sulhu ba, ana iya fuskantar wani sabon umarni na rufe iyakokin daga kasashen na ECOWAS kamar Najeriya da kuma Benin. Ko da yake wasu na ganin cewa rufe wasu iyakokin na daga cikin taka-tsan-tsan, ganin zaman tankiya da sababbin hukumomin na Nijar ke yi da kashen na ECOWAS.