Somaliya ta kori jakadan Habasha
April 4, 2024Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan da ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta gana da hukumomin yankin Puntland na Somaliya mai cin kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai, wandanda a ranar Lahadin da ta gabata suka nuna rashin amincewa da hukumomin Mogadishu tare da neman cikakken 'yancin yankin.
Karin bayani: AU ta ja hankalin Habasha da Somaliya
A baya dai kasashen biyu makwabta da ke yankin kahon Afrika, na takun saka ne kan yankin Somaliland wanda ya balle daga Somaliya tare kuma da kulla alaka da Habasha, lamarin da ya haifar da rikicin diflomasiyya mai zafi.
Karin bayani: Somaliya ta yi tir da yarjejeniyar Habasha da Somaliland
Wannan lamari ya kai manyan kasashen duniya irin su Amurka da China da kuma kungiyar AU ga yin kira ga kasashen biyu da su gaggauta yi wa tubkar hanci, don kaucewa bata kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin su.