1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Spain ta ceto 'yan ci-rani 516 daga Afirka a tsibirin Canary

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 6, 2024

'Yan ci-ranin da suka hada da jarirai da kananan yara, sun shaidawa hukumomin Spain cewa 12 daga cikinsu sun mutu a kan hanya

https://p.dw.com/p/4gkl6
Hoto: Europa Press/AP Photo/picture alliance

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Spain ta samu nasarar ceto 'yan ci-rani 516 'yan Afirka a tsibirin Canary, lokacin da suke yunkurin tsallakawa kasar ta cikin kwale-kwalen ruwa guda 5.

karin bayani:An gano gawarwakin 'yan ci-rani guda biyu a cikin jirgin ruwan da ke dauke da mutane sama da 200 a Spain

'Yan ci-ranin da suka hada da jarirai da kananan yara, sun shaidawa hukumomin Spain cewa 12 daga cikinsu sun mutu a kan hanya, inda suka jefa gawarwakinsu cikin ruwa, yayin da wata mata kuma ta haihu a kan hanya.

Karin bayani:'Yan Najeriya sun makale a karkashin jirgin ruwa har zuwa Spain

Ma'aikatar harkokin wajen Spain ta ce a watanni biyar na farkon wannan shekara ta 2024, 'yan ci-rani dubu ashirin da daya ne suka shiga kasar ta cikin ruwa, lamarin da ke nuna karin kashi 136 cikin 100 a kan na bara.