Matsalar jin-kai na karuwa a Sudan
June 12, 2023Jim kadan bayan cikar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 24 a tsakanin bangarorin da ke yakar juna a Sudan din, wani sabon rikici ya sake barkewa. Wannan dai na kara firgita al'ummar kasar da masana da ke cewar a kullum fadan na kara kamari wanda ake fargabar ka iya kai kasar ga wani mummunan yanayi. Kawo yanzu dai gaza hango karshen wannan rikici na Sudan, bayan kwashe sama da makwanni takwas ana gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin da ke gaba da juna. Sannu a hankali Sudan ke tunkarar matsalar karancin abinci ko baya ga sauran matsaloli, a cewar guda daga cikin shugabannin wata cibiyar bincike a kasar Muzan Alneel da ta ce ka iya kai ga barkewar fada a tsakanin fararern hula saboda tsananin yunwa. Wannan rikicin na Sudan da aka fara tun a tsakiyar watan Afirilun wannan sh. Akwai matsalolin rashin ruwan sha da abinci da katsewar hasken wutar lantarki, kana fannin lafiyar kasar na cikin wani mawuyacin hali.
A cewar ma'aikatar lafiya ta kasar rikicin ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane sama da 800 ya zuwa yanzu, yayin da wasu 6000 suka jikkata. Sai dai wasu na ganin adadain ya haura haka, saboda mutane da dama ba sa zuwa asibiti kuma ana ci gaba da tsintar gawarwaki a kan titunan kasar musamman a yankin Dafur na Sudan din da rikicin tuni ya rikide ya zuwa na kabilanci. A cewar Theodore Murphy babban darakta a Majalisar Gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai a kan shirin Afirka, wani babban dalilin da ya sa wannan rikicin ke kara rincabewa shi ne yana tayar da tsohon ciwon da ke zukatan al'umma. Hager Ali wacce ke bincike a wata cibiya ta Jamus mai suna Think tank Giga, na ganin karkata akalar rikicin ya zuwa na kabilanci na kara wa rundunar RSF tagomashi. Tana mai cewa sun sauka daga turbar da fadan ya samo asali, kuma fadan kabilanci a ire-iren wadannan kasashe na da hadari.