Sunayen fitattu a harkar fina-finan zamani a Afirka
Kama daga Nollywood zuwa Netflix, wadannan masu shirya fim, sun yi tasiri a duniyar fina-finai da sabbin labarai da dabarun kwalliya.
Wanuri Kahiu
An haife ta a Nairobi a shekarar 1980, daraktar ta yi nasarar a duniya a 2018 da fim din "Rafiki". Shi ne fim din Kenya na farko da aka nuna a bikin Cannes. Wasan kwaikwayon game da soyayyar mata biyu 'yan madigo, wanda aka haramta nuna shi a Kenya. Yanzu haka Kahui ta nufi Hollywood, inda za ta shirya fim din "The Thing about Jellyfish".
Kunle Afolayan
Daraktan dan Najeriya na daya daga cikin muhimman wakilai a sabon Ciniman kasar (New Nollywood), wanda ke tattare da basira mai rikitarwa, wanda ke bukatar kasafin kuɗi mai yawa. Shahararren fim din Afolayan mai suna "The Figurine - Araromire" (2009), na daya daga cikin fitattun fim da suka yi nasara a Najeriya, wanda ya zama a matsayin jigon tafiyar.
Abderrahmane Sissako
Fina-Finan Sissako suna magana ne kan muhimman batutuwa kamar su dunkulewar duniya da ta'addanci da kaura. Darakta kuma mai shirya fim, wanda aka haifa a Mauritania kuma ya girma a Mali, yana ɗaya daga cikin shahararrun masu shirya fim daga yankin Afirka da ke Kudu da Sahara. An zabi fim dinsa na "Timbuktu" (2014) a bikin fina-finai na Oscars kuma ya ci kyaututtuka a Césars da Cannes.
Kemi Adetiba
Mai shirya fina-finan Najeriya, wacce kuma ke yin jerin shirye-shiryen TV da bidiyon wake-wake, fitacciya ce a kamfanin fim na Nollywood a Najeriya, da ke zama na biyu mafi girma bayan na Indiya. Sabbin fina-finan Adetiba sun samu karbuwa. Ta na shirya fim dinta na gaba, wanda zai biyo bayan fitaccen fim ɗinta na "King of Boys", kuma za a yi shi ne musamman don Netflix.
Philippe Lacôte
Daraktan fim daga Ivory Coast kwanan nan ya gabatar fim dinsa na farko "La Nuit des Roies" (2020) a bikin fina-finan duniya. Fim din, wanda ke tunatar da labarin littafin nan na dare 1001, da ke ba da labarin wani mai laifi "Zama", wanda aka tura gidan kurkukun "La Maca" a Abidjan. Don tsira a can, dole ne ya zama mai ba da labari.
Machérie Ekwa Bahango
Sabuwar baiwa kuma mai hazaka: Daraktar mai shekaru 27 daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta fara ganin nasara a fim dinta "Maki'La" a bikin nuna fina-finai a Berlin a cikin 2018. Matashiyar wacce ta koyi aikin da kanta, ta kwashe shekaru uku ta na aikin fim dinta na farko, wanda ya bada labarin wasu yara kanana a titunan Kinshasa. Ya lashe babbar kyautar "Ecrans Noirs" a Kamaru.
Moussa Touré
Moussa Touré mai shirya fim ne kuma marubucin labari ne a Senegal, ya jima ya na taka rawa a duniyar wasannin kwaikwayo a Afirka. Galibin fina finansa na da alaka da siyasa. Touré ya bayyana fim dinsa mai su na "La Pirogue" (2012), da ke ba da labarin balaguron 'yan cirani daga Afirka zuwa Turai ta cikin ruwa, a matsayin "tozarta gwamnatin Senegal".
Tsitsi Dangarembga
An haife ta a Zimbabuwe a 1959, ba wai fim kadai ta ke shiryawa ba, ta sa samu nasara a rubuta litattafai da da labarai, ciki har da fim dinta na "Neria" (1993), wanda ya zama fim din da aka fi kallo a Zimbabuwe. A shekarar 2020, an kama Dangarembga a birnin Harare lokacin zanga-zangar adawa da rashawa na gwamnati. Sai dai tuni aka sake ta.