1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarbar ban girma ga kungiyar Super Eagles

February 13, 2024

Kasa da sa'o'i 48 da kammala gasar cin kofin kasashen Africa na kwallo na kafa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa kungiyar Super Eagles ta Najeriya tarbar sarakuna a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.

https://p.dw.com/p/4cMal
Najeriya| Kwallon Kafa | Super Eagles | AFCON | Bola Ahmed Tinubu | Kashim Shettima
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa da tawagar 'yan wasan kasarHoto: Ubale Musa/DW

An dai kai ga hotuna an kuma sha hannu, ko bayan jerin kyautukan filaye da gidaje a Abuja, ko bayan lambar girman MON duk a kokarin karrama 'yan wasan na Super Eagles da suka zo na biyu a gasar wasan kwallon kafa ta kasashen Afirka AFCON. A wani kwarya-kwaryan biki a fadar gwamntin kasar da ke a Abuja dai, gwamnatin kasar ba ta boye farin cikinta kan rawar 'yan kwallon a gasar da ke zaman mafi tasiri a nahiyar. Duk da cewar dai sun gaza daukar kofin, rawar Super Eagles din na zaman kokarin samun sanyi a banagren 'yan mulkin da ke dada fuskantar karin matsin lamba cikin kasar a halin yanzu. In har masu takama da takun ledar sun burge Abujar, ita ma kyautar daga dukkan alamu ta burge masu takun ledar da ke fadin son barka.

Najeriya| Kwallon Kafa | Super Eagles | AFCON
'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya Super EaglesHoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

#b#Sai dai kuma a yayin da masu taka ledar ke murna, wani abun da ya dauki hankalin zaman shi ne bita da kullin da ake zargin yi wa wasu 'yan wasan na Super Eagles bayan kammala gasar. Sai da ta kai ga kyaftin dinsu Ahmed Musa tashi a tsaye, domin kare Alex Iwobi da ya sha suka kan rawar da ya taka yayin gasar. A cikin watan gobe na Maris ne dai, kungiyar take shirin dorawa a cikin kamfen din neman taka rawa a gasar wasan kwallon kafa ta duniya. Kuma a fadar Ibrahim Musa Gusau da ke zaman shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar NFF, karramawar na zaman kwarin gwiwar dorawa a cikin neman kai wa ya zuwa gasar da ke da tasirin gaske. Abun jira a gani dai na zaman nisan harkar wasan da ga dukkan alamu, ke zaman igiya guda daya da ke daure da Tarayyar Najeriyar a halin yanzu.