1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka na son taka rawar gani

Mouhamadou Awal Balarabe AH
July 17, 2023

wakilan Afirka a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa na mata karo na tara da suka hada da Zambiya da Maroko da Najeriya da kuma Afirka ta Kudu sun shirya kare martabar nahiyarsu.

https://p.dw.com/p/4U0Av
Kungiyar wasan Najeriya mata Super Falcons
Kungiyar wasan Najeriya mata Super FalconsHoto: Tobi Adepoju/Shengolpixs/IMAGO

Tauraruwar wasan tennis ta nahiyar Afirka Ons Jabeur ta sha kashi a wasan karshe na rukunin mata na Wimbledon, wanda ke zama Grand Slam na uku da mai matsayi na shida a duniya ta baras a tarihinta. Duk da nasarar yin waje road da manyan giwayen tennis na duniya Elena Rybakina a matakin kwata fainal da Aryna Sabalenka a wasan kusa da na karshe, amma kuma 'yar Jamhuriyar Czech Vondrousova mai matsayi 46 a duniya ta kwance wa Jabeur zani a kasuwa da rukunin ci 6-4, 6-4. 'Yar kasar Tunisiyar mai shekaru 28 a duniya ta zubar da hawaye saboda bakin ciki, amma ta yi alkawarin sake jan damrara don ta dawowa da karfinta "Ina ganin cewa wannan ne rashin nasara da ya fi zafi a rayuwata! Da farko ina taya Marketa da tawagarta murnar rawar da suka taka a gasar, ke 'yar wasa ce da kika san abin da kike yi, kuma ina alfahari da abin da ki ka samu. Wannan wasan karshe ne da zai yi wuya a manta da shi. Amma ba zan yi kasa a gwiwa ba, zan dawo da karfi'' Ons Jabeur ce 'yar wasa ta farko daga kasashen Larabawa da ta kai wasan daf da na kusa da na karshe na Grand Slam a gasar Australian Open a shekarar 2020, kuma ta farko da ta shiga rukunin 'yan tennis 10 mafi bajinta a jerin da WTA ke fitarwa. A shekara ta 2022 ga misali, ta tashi daga lamba 6 zuwa lamba biyu na duniya a rukunin mata. A rukunin maza kuwa, laya ba ta yi wa Novak Djokovic na Sabiya kyaun rufi ba saboda Carlos Alcaraz na Spain da ke da matsayi na daya a fagen tennis a duniya ya doke shi a rukunonin wasanni biyar da suka yi. Wannan dai ya sa Alcaraz cika mafarkinsa na harbin tsuntsaye biyu da dutse daya: na farko doke Djokovic da ya taba lashe gasar Wimbledon sau da dama, tare da lashe babbar gasar Slam na biyu a rayuwarsa baya ga wanda ya samu yana da shekaru 20 a duniya.

Shirin kammala gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya

Film | Running Against the Wind
Hoto: R&B FILM

Kwanaki uku gabanin kammala gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta masu bukata ta musamman a birnin Paris na Faransa, 'yar Aljeriya Safia Djelal ta kafa tarihi, inda ta harbin nauyi a keken guragu na maki 11.57. Hasali ma bayan gadan kanta da ta yi a matsayin wacce ta lashe zinare, ta inganta tarihinta na baya da centimita daya. Ita kuwa kasar Japan ta lashe zinare a tseren mita 4x100 na duniya, bayan soke cancantar da Kanada da ta zo na daya a wasan karshe. Ita kuwa Yasin Khosravi 'yar kasar Iran ta inganta bajintarta a harba nauyi inda a wannan karon ta kai mita 16.01. A fannin masu laruruwar kwakwalwa kuwa, Jose Gregorio Lemos ne yaA yammacin wannan Litinin ne za a kawo karshen gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta masu bukata ta musamman, wadda ke zama zakaran gwajin dafi na gasar Olympics da za ta gudana a shekara ta 2024 a kasar ta Faransa.  Chaine ce ta mamaye gasar a yawan jimillar lambobi, ita kuwa Brazil tana biya mata baya yayin da Amirka ke a matsayi na uku

Kasashen Afirka na son taka rawar gani a gasar kwallon kafa ta duniya

DW l Vier afrikanische Teams kämpfen um die Frauenfußball-Weltmeisterschaft
Hoto: Olisa Chukwumah/DW

A daidai lokacin da ya rage kwanaki uku a fara gasar cin kofin duniya ta kwallon mata a Ostireliya da New Zealand, tawagar 'yan matan Jamus ta isa sansanin sansaninta da ke  arewacin Sydney, inda a rukuninta za ta fafata da Maroko a ranar 24 ga Yuli. Ita kuwa Ostireliya mai masaukin baki ta doke Faransa a wasan sada zumunci na karshe da ci daya mai ban haushi a birnin Melbourne. A daya bangaren kuwa, a wani hali da ba a saba ganin irinsa ba, 'yan Ireland sun fice daga filin wasa na Brisbane  bayan an shafe mintuna 23 ana wasa da Kwalambiya, suna zargin 'yan wasan na Kwalambiya da amfani da karfin tuwo, lamarin da zai iya haddasa su rauni tun kafin a shiga gasar gadan-gadan. Su ma dai kasashe hudu da za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya ta mata karo na tara da suka hada da Zambiya da Maroko da Najeriya da kuma Afirka ta Kudu sun shirya kare martabar nahiyarsu. Hasali ma dai. Kungiyar kwallon kafan mata ta Super Falcons ta Najeriya na kan gaba a ‘yan wasan da ke wakiltar Nahiyar Afrika kasancewar ta shiga  kofin kwallon kaf ana duniya na ‘yan mata ba sau daya ba ba sau biyu ba. To amma shirye-shiryensu ya yi daidai da matsayinsu na giwayen kwallon mata na Afirka? kuma wace damar da suke da ita a gasar ta wannan shekara a matsayinsu na gwarajen Afrika?

Hada-hadar 'yan wasan kwallon kafa na lokacin bazara.

EURO2020 I Finale I England v Italien
Hoto: Laurence Griffiths/REUTERS

Manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai na ci gaba da gudanar da hada-hadar 'yan wasan na lokacin bazara. Kuma na baya-bayannan da ya fi daukar hankali shi ne cinikin da jaridu suka yayata cewar Manchester United na gab da kammalawa da mai tsaron gida dan asalin Kamaru Andre Onana daga Inter Milan bayan sakamakaon yadda Erik ten Hag ya kwallafa rai a kansa. Onana dai ya taba wasa karkashin manaja ten Hag yayin zamansa a Ajax Amsterdam na shekaru 7 kafin ya koma Inter Milan, inda ya nuna kwarewa a  Serie A. Ita kuwa Liverpool na sa ran sayen dan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips domin ya maye gurbin Fabinho wanda ya kama hanyar komawa kasar Saudiyya. A nata bangaren, Inter Milan ta Italiya ta kama zawarcin Alvaro Morata na Atletico Madrid gadan-gadan, baya ga dan wasan Arsenal Folarin Balogun dan asalin Amurka..Kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke Amurka ta gabatar da sabon dan wasanta na gaba Lionel Messi gaban dimbin magoya baya a fili wasa na Fort Lauderdale duk da jinkirin da aka samu sakamakon rashin kyawun yanayi. A watan da ya gabata ne tsohon dan wasan na PSG ya sanar cewa zai koma kungiyar ta Florida da ke bugawa a Lig MLS ta Arewacin Amurka. Amma Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau bakwai a rayuwarsa ya  ya yi alkawarin bayar da gudunmawa domin ciyar da Inter Miami gaba kamar yadda ya yi a wasu kungiyoyi a baya. Lionel Messi zai fara yi wa Inter Miami tamaula a karawar da za ta buga a League Cup da Cruz Azul ranar 21 ga watan Yulin 2023. Bisa ga kwantiragin da ya sa hannu a kai dai, Messi mai shekaru 36 da haihuwa zai teka leda na tsawon shekaru biyu ne a Inter Miami, kuma abin farin cikin a gare shi, shi ne damawa da zai yi da tsohon abokin wasansa Sergio Busquet da ya koma Inter Miami bayan da ya raba gari da Barcelona.