Kotu ta soke sabbin sarakunan Kano
November 21, 2019Galibi dai mutane da dama sun bayyana cewar siyasa da kuma rikicin da ke tsakanin gwamna Ganduje da sarkin Kano Sarki Muhammadu Sanusi na 2 wadannan abubuwan sun taka rawa wajen kirkirar wadannan sabbin masarautu wadanda za su yi goggaya da sarkin Kano. Kotun karkashin alkali Usman Na Abba ta ayyana cewar dokar da majalisar dokokin Jihar kano ta dauka wacce ta bai wa gwamnati damar raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar, haramatacciya ce domin ba a bi ka'idojin da suka dace ba wajen girka wannan doka.
Shin mi zai iya biyo bayan yanke hukuncin da kotu ta yi, gwamnatin Jihar Kanon za ta martaba dokar
Yayin zartas da hukuncin alkalin ya bayyana cewar dukkanin hanyoyin da majalisar ta bi wajen yin dokar ba su da tushe don haka ta rushe wnanan doka. To amma wane mataki gwamnati za ta dauka a kan wannan hukunci da ake ganin ya mayar musu da hannun agogo baya. .
Barrister Ibrahim Muktar ya bayyana cewar za su dauki mataki amma ba za su bayyana matakin ba sai sun kammala tattaunawa da sauran lauyoyi. A karshen zaman kotun dai alkali Usman Na Abba ya bayyana cewar akwai dama ga wanda duk bai aminta da hukuncin ba, domin ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da ke Kaduna.