1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Ta'adin da ambaliya ta yi a Najeriya da Nijar

October 20, 2022

A yayin da ruwan sama ke zuba kamar da bakin kwarya a sassan Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ambaliyar da ake gani a yanzu a cikin kasar na zama mafi girma daka taba gani.

https://p.dw.com/p/4ITus
Nigeria Überschwemmung in Lokoja
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Ambaliyar ruwa ta zama kalubale a kusan duk shekara ga jama'a a yankunan Afirka, ganin yadda take shafe gonakin noma, ko rushe gidaje ba tare da al’ummar da ke cikin wannan yanayi na samun cikakkakiyar kulawa ba. Gwamnatocin kasashen dai na cewa a bana sun soma nazari don samar da inshora don kawo sauki ga wadanda ibtila'in ya afka wa.

A yayin da ruwan sama ke cigaba da zuba a sassan Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ambaliyar da ake gani a yanzu a cikin kasar na zama mafi girma da aka fuskanta a sama da shekaru 10.