Tababa a kan sakamakon zaben Togo
August 1, 2013Bisa wannan sakamako dai jam'iyya mai mulki ta Union of the Republic ce ta lashe zaɓen da kujeru 62 cikin 91, matakin da zai baiwa iyalin shugaban ƙasa Faure Gnassinbe damar dawwama a kujerar shugabancin ƙasar.
Haɗakar jamiyyan adawan sun yi zargin cewa an sami kurakurai tun kafin ma a kammala ƙidayar ƙuri'un da yammacin lahadi, ranar litini kuma Agbeyome Kodjo wani jigo a haɗakar jamiyyun ya kira ya ce sakamakon zaɓen ungulu ne da kan zabo kuma Eric Dupuis mamba a ƙungiya ya yi ƙarin bayani.
Ya ce: "Haɗakar Jamiyyun CST sun yi Allah wadai da wannan sakamako da ƙwaƙwarar murya sakamakon baki ɗaya, domin sakamakon zaɓen 'yan majalisar dokokin da aka gudanar ranar 25 ga watan Yulin shekarar 2013 wadda hukumar CENI ta gabatar. Gurguntaccen tsarin da aka yi amfani da shi, ya nuna cewa tun a lokacin shirye-shirye aka yi zamba, cin hanci da sayar da mutuncin mutane, tsoratar da jama'a, rikici da rashin mutunta dokoki da sauran abubuwa ne suka taru suka mamaye tsarin ke nan a duk fadin ƙasar."
To sai dai masu sanya ido na Ƙungiyar Tarayyar Afirka da Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS sun ce an gudanar da zaɓe a yanayin da ya dace. Ofishin jakadancin Amirka da ke Togo ya aikar da gaisuwar taya murnarsa ga hukumar zaɓe musamman sabnoda nasarar da ta yi na gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali. Ita ma a nata ɓangaren hukumar zaɓen mai zaman kanta na CENI ta ce ta gamsu da yadda ta kammala aikin da ke gabanta cikin yanayi na kwanciyar hankali kamar yadda mataimakin shugaban hukumar zaɓe Jean Claude Homawo ya bayyana:
Ya ce "zamu iya cewa Togo babban mataki, saboda mun tabbatar cewa a lokacin zaɓen mun cimma matsayar da kowa ya amince burin ya kasance na tallafawa Togo ne."
Wannan zaɓe dai ya zo ne bayan da aka shafe watanni ana jinkirtawa inda 'yan adawa suka buƙaci a gabatar da mahimman sauye sauye, yawancin masu zanga-zanga dai 'yan sandan ko ta kwana sun tarwatsa su suna amfani da hayaƙi mai sanya hawaye inda a waje guda kuma gwamnati ta tsare wasu mutane 35 yawancinsu 'yan adawa waɗanda ake zargi da sanadiyyar ƙonewar wasu kasuwanni a ƙasar. Ranar alhamis ne dai aka sako 13 daga cikinsu amma sauran na nan a tsare.
Gilbert Bawara shi ne ministan cikin gida wanda ya kwatanta zaɓen a matsayin abun koyi ga sauran ƙasashe.
Ya ce: "A ƙarshe zaɓe ne wanda ya sami hadin kan ɓangarori wanda kuma bai bar kowa a baya ba a ranar zaɓe komai ya tafi yadda ya kamata bayan da aka gudanar da yaƙin neman zaɓe wanda aka yi cikin kwanciyar hankali, ranar zaɓe ma ba a sami manyan matsaloli ba, gaba ɗaya za a iya cewa tsari ne da ke zaman wani abun koyi."
Ita dai gwamnatin ƙasar wadda al'ummarta ke da yawan milliyan shidda ta jaddada cewa a shirye ta ke ta gudanar da sauye-sauye kuma tana aiki tuƙuru wajen inganta tattalin arziƙin ƙasa da samar da ababen more rayuwa, abun da 'yan adawa suka musanta.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar