1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar kasuwar magani a Kano

Nasir Salisu Zango
January 17, 2023

Bayan tsawon lokaci na muhawara tsakanin gwamnatin Kano da 'yan kasuwar magani, gwamnati ta sanya ranar da 'yan maganin za su tashi daga inda suke hada hada domin tarewa a sabon mazauninsu.

https://p.dw.com/p/4ML8O
Hoto: Klaus Rose/picture alliance

An shafe shekaru ana takaddama tsakanin gwamnatin Kano da ‘yan kasuwar magani da galibi ke kasuwancinsu a kasuwar sabon gari, daga bisani wannan zaman doya da manja ya sa 'yan kasuwar yin sansani a wasu kasuwanni dake titin Niger street inda suka ci gaba da hada hadar maganin. To amma yanzu gwamnatin kano ta ce ta kammala shirye shirye domin mayar da su mutsuguni na dindindin a kasuwar Dangwauro kan titin zuwa Zaria.

An dade dai ana zargin yawancin masu sayar da magani da cinikin miyagun kwayoyi wanda ya sa a baya jihar ta dade a kan gaba na yawan matasa da ke ta'ammali da miyagun kwayoyi. Kwmaishinan kasuwanci na jihar Kano Barrister Ibrahim Muktar ya ce bayan miyagun kwayoyi ana zargin masu maganin da sayar da gurbtattun magunguna.

To amma da yawan 'yan kasuwar na ganin cewar an yi hanzarin tilasta musu tarewa a kasuwar don kuwa akwai ayyukan da ba a kammala ba a saboda haka suke rokon a dage tarewar.

Pharmcist Ahmed Ibrahim Yakasai shine tsohon shugaban majalisar masu hada magunguna ta Nigeria, ya ce ko kusa babu dalilin dage wannan tariya don kuwa barnar da ake yi a yanzu ta shallake hankali.

Yanzu haka dai gwamnatin Kano ta jadadda cewar babu gudu ba ja da baya wajen tarewa a wannan kasuwa a ranar 10 ga watan Fabrairu, kuma gwamnatin ta ce ta shirya sanya kafar wando daya da duk wanda ya bijire wa umarnin amma fa duk da haka wasu 'yan kasuwar na gunagunin cewar komawa a yanzu zai kassara tattalin arzikin dubban mutane.