Tallafa wa kasashen yankin Tafkin Chadi
February 24, 2017Wannan taro wanda shi ne irinsa na farko ya zo ne a dai-dai lokacin da yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ke cikin tsananin bukatar tallafi musamman na abinci da magunguna da kuma ruwan sha da ma muhalli, ga mutane sama da miliyan biyu da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu. Har kawo yanzu kokarin da kungiyoyin agaji na kasa da kasa da da ma hukumomi ke yi na magance matsalar yunwa da kuma karancin magunguna, bai kai ga shawo kan matsalar ba wata kila saboda girman matsalolin da rikicin na Boko Haram ya haifar. Malam Ibrahim Yusuf guda ne daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin fararen hula a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya a ganinsa shiyyar na bukatar abubuwa masu daman gaske.
Ana zargin hukumomi a Najeriya da kasa samar da isassun kudaden da za a kula da wanan yankin da rikicin Boko Haram ya dai-daita abin da ake ganin shi ne ya kara dagula al'amura. Ko a makon da ya gabata kwamitin da shugaban Najeriya ya kafa don sake gina shiyyar Arewa maso Gabashin kasar da rikicin Boko haram din ya lalata, sun koka kan karancin kudaden da aka ware a kasasfin kudi domin kulawa da 'yan gudun hijira da kuma maganace matsaloli da yanzu haka yankin ke ciki. Sanata Ali Ndume wanda ya jagoranci 'yan kwamitin a wata ziyara da suka kai Maiduguri, ya nuna yadda kungiyoyin agaji na kasa da kasa ke ware makudan kudade sama da yadda Najeriya ke ware wa domin kula da kuma shawo matsalolin da al'ummar yankin ke ciki a halin yanzu.
Yayin da ake kokarin tara wannan tallafi da kasar Jamus tare da hadin gwiwar kasar Beljiyam ke shirya wa kungiyoyin fararen hular, sun nemi a dauki matakai na sa ido a kan yadda za a yi amfani da wannan tallafi domin kauce wa yin sama da fadi da su kamar yadda aka gani a baya, inda kayan tallafi suka yi batan dabo. Sai dai gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya bayar da tabbacin ce wa duk wani tallafi da aka kawo za su yi bakin kokarinsu wajen ganin an yi gaskiya wajen rabon agajin.