Najeriya: Shirin sayar da abinci da rangwame
July 24, 2023kama daga babban bankin CBN ya zuwa ga rumbunan ajiyar na gwamnatin kasar 33 dai 'yan mulkin Najeriyar sun ce suna da akalla buhu miliyan 50 da nufin rage radadin da ke neman zauta 'yan kasar a halin yanzu. Jihohin kasar 36 ne dai za su jagoranci shirin da a karkashin sa za'a sayar da abinci da sauki ga masu bukata a fadar Inuwa Yahaya da ke zaman gwamnan Gombe kuma shugaba na kungiyar gwamnonin arewacin kasar in da barazanar ta abinci ke zaman mai girma ya ce shirin zai taimaka. Duk da cewar babban bankin kasar na CBN ya ce ya yi nisa cikin shirin tare da sauyin buhuna da nufin kaucewa wasoso cikin kasar da ke karatun ni yasu, akasin alkawarin 'yan mulkin babu alamun fara rabon a mafi yawa na wurare. Kabir Ibrahim dai na zaman shugaban kungiyar manoman tarrayar Najeriyar ta AFAN da kuma ya ce babu alamun fara shirin a ko'ina cikin kasar a halin yanzu.
Ko gwamnatin Najeriyar za ta cika alkawarin da ta dauka zuwa ga al'umma
Babban rikicin dai ya zuwa yanzu na zaman iya kai wa ya zuwa cika alkawarin taimaka wa mutane miliyan 50 da ke da bukata ta talalfi cikin kasar a halin yanzu. Majioyyi dai sun ce ko bayan tan dari biyu ko kuma buhu miliyan daya da babban bankin CBN ke takama da shi. Mohammed Magaji da ke sana'ar noman, abincin da ke a rumbuna na gwamnatin bai taka kara ba balle kai wa ya zuwa ga bukatar miliyoyin na 'yan kasar da ke bukatar sauki. Akalla tan dubu 72 ne dai ake zargin daka wasoso a karkashi na tsohuwa ta gwamnatin in da mafi yawan hatsin ya koma makami na siyasa cikin kasar.