Borno: Buhari ya kaddamar da shirin agaji
August 18, 2022Shirin dai wanda shi ne irinsa na farko zai bada tallafi ne ga mutanen da ke cikin kunci wadanda matsalolin tsaro da na dumamar yanayi suka shafa.
Baya ga kudaden tallafi da aka bai wa mutane kusan dubu takwas wanda ake sa ran za su yi amfani da su wajen yin jari ko kuma wasu abubuwan da za su taimaka wa rayuwarsu akwai kuma kimanin mutane dubu hamsin da za a basu tallafin kayan abinci.
Wannan aikin jinkai wani bangare ne na bukukuwan ranar Majalisar Dinkin Duniya kan taimakon jinkai ga al'umma a fadin duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya zama dole a dauki matakin taimakawa wadan nan bayin Allah wadanda suke cikin mawuyacin hali sakamakon rikici da kuma matsalolin dan Adam ya haddasa.
Ya ce a matsayin gwamnati mun zabi wannan rana domin sake jaddada manufofi da kudirorinmu wajen rage illar dumamar yanayi da sauran matsalolin da suka addabi al’ummar Najeriya ta hanyar samar musu da tallafin da zai taimaka wa rayuwarsu saboda su rayu cikin mutunci da kwanciyar hankali
Kusan dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin jinkai sun samu halartar kaddamar da wannan shiri jinkai inda aka yi jawabai na karfafa gwiwa ga masu aikin jinkai da kuma wadanda ake tallfawa da ayyukan jinkan.
Mr Matthias Schmale shi ne babban jami’in da ke kula da harkokin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya.
"Mun zaku mu ga an kawo karshen wannan mummunan yanayi da al’umma suka shiga sanadiyyar ayyukan dan Adam. Mafita guda ita ce a samar da zaman lafiya”
Shi kuwa gwamman jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum cewa ya yi sai an binciko tare da magance tushen rikicin da kuma abun da ya haifar da shi wanda ya hada da matsalar dumamar yanayi.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke ziyarar aiki a jihar Borno karo na uku a cikin shekara guda ya yi amfani da damar ziyarar wajen kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar.