1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaTanzaniya

Kula da jarirai bakwaini a Tanzaniya

September 12, 2023

A kan haifi jariran da ba su isa haihuwa ba da ake kira da bakwaini sama da dubu 300 duk shekara a Tanzaniya. Sai dai sama da kaso 70 na rasa rayukansu a kasa da sa'o'i 48, sakamakon rashin kayan kula da lafiyarsu.

https://p.dw.com/p/4WG4m
Tanzaniya | Jarirai | Bakwaini | Lafiya
Ceto rayuwar jariran da aka haifa a matsyin bakwanin a TanzaniyaHoto: DW/H. Bihoga

Karuwar mutuwar jarirai da ake samu a Tanzaniyan dai, na da nasaba da matsalar rashin ingantattun kayayakin aikin kula da lafiyarsu da kusan daukacin asibitocin kasar ke fama da ita. Ya zuwa yanzu za a iya cewa Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta himmatu wajen kawo karshen wannan matsalar, inda ministar lafiya ta Tanzaniya Ummy Mwalimu ta sanar da cewa, an samar da sama da dakunan kula da bakwaini 180 a asibitocin fadin kasar kari a kan 14 da ake da su a baya. Sai dai wata likita Dakta Maria Bitwalo ta ce duk da haka ana samun karuwar jariran da ke mutuwa, amma a nasu bangaren suna kokarin ganin adadin ya sauka sosai. A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, sama da jarirai miliyan 15 ne ke rasa rayukansu a duk shekara mafi akasarinsu bakwaini.