Tarihin Mataimakin shugaban Najeriya Muhammadu Namadi Sambo
May 20, 2010Tarihin Tsohon gwamnan jihar kaduna kuma sabon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Namadi Sambo.
Shidai Sabon mataimakin shugaban ƙasa Arc. Namadi Sambo an haife shi ne a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 1954 a garin Zariya ta jihar kaduna. Kuma ya fara makarantar Firamare ne a Baptist primary da ke kakuri kaduna da kuma Makarantar firamare ta Kobi a jihar Bauchi a shekaran 1959.
Daga shekarar 1967 zuwa 1971 ya halarci makarantar sakandare ta Alhudahuda dake Zariya. Alhaji Namadi Sambo ya halarci jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya karanci fannin Zanen taswiran gine-gine daga shekarar 1973 zuwa 1978.
Sabon mataimakin shugaban ƙasar yayi aikin yiwa ƙasa hidima a shekarar 1979 a ma'aikatan aiyuka da gidaje da ke jihar Oyo. Ya kuma riƙe muƙamin kwamishinan Aiyuka da sufuri da gidaje a 1988, Kafin ya kafa kanfanin kansa.
Alhaji Namadi Sambo yana da aure da 'ya'ya shida. A ranar 18 ga wannan watan ne majalisar dokokin Najeriya ta amince da naɗin sa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, kana aka rantsar dashi a ranar 19 ga watan Mayun ta 2010.Kuma shine mataimakin shugaban ƙasa na 13 a tarihin Najeriya.
Karin bayani:KDSG
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Zainab M. Abubakar