Shara barazanar birnin Fatakwal
December 18, 2018Birnin Fatakwal, mai arzikin danyan mai a yankin Niger Delta, haka kuma birni ne da ya samo tarihi na kyan tsari da kuma tsafta, inda ma wasu ke bayyana shi da zamowa Turai a Najeriyar, kuma tsaftar ke sawa ake masa lakabi da suna Garden City wato birni mai lambun sha'awa.
To sai dai a yanzu bisa la'akari da yadda yanayin birnin ke samun koma baya a fannoni musamman tsaftarsa da aka sani, ta yadda kusan ko ina baka raba shi da datti da tulin shara, ga tarin masu larura ta tabin hankali da ke gararamba tare da tattara shirginsu kan titunan birnin daban-daban, kama daga manya-manyan tituna na fita kunya zuwa kanana.
Dangane da yadda wannan kawataccen birni ke sauyawa a yanayin kyawunsa zuwa wata kama ta Allah wadai, kungiyoyin dalibai daga manyan makarantu daban-daban a jihar, masu kuma fafutukar kare muhalli, da ke da lakabi Students Volunteer Advocacy For Clean Environment a Turance suka gudanar da wata zanga zangar lumana a baya-bayan nan, domin kokawa tare da jan hankulan hukumomin jihar Rivers din kan yadda birnin ke dada kazancewa.
Duk da mahukunta sun ajiye motoci na kwashe shara, amma dai sun yi karanci don haka ake ganin akwai bukatar ganin al'umma sun tashi tsaye wajen kula da muhalli da yin tsafta.