Kokarin tabbatar da hadin kai a jam'iyyar APC
October 10, 2018Har ya zuwa yanzu dai kawuna na rabe acikin jam'iyyar APC mai mulki bayan zabe, kuma a wasu jihohin irin su Zamfara ana ma hasashen yiwuwar tafiya zaben ba tare da 'yan takara a zaben gwamna da kuma 'yan majalisar dattawa da na wakilai ba. To sai dai kuma wani taron gwamnonin na APC da Shugaba Muhammadu Buhari, na neman hanyoyin kai karshen matsalolin da ke zaman barazana mai girma da ke iya shafar makomar jam'iyyar a zaben da ke tafe.
Ya zuwa ranar wannan Laraba dai jam'iyyar ta APC ta aike da wasikar koke ya zuwa hukumar zaben Najeriyar na da nufin nuna adawarta a bisa matsayin hukumar cewar ba ta da damar tsaida 'yan takara cikin jihar ta Zamfara mai tasiri. Kuma a fadar Abdullahi Umar Ganduje da ke zaman gwamnan jihar Kano daya kuma a cikin mahalarta taron, ya ce APC ta yi imanin ba ta da matsala a jihar ta Zamfaran a halin yanzu.
Akwai dai tsoron yiwuwar lalacewar lamura ga masu tsintsiyar da ke fuskantar sake dorawa a cikin mulki na kasar amma kuma ke fuskantar barazana mai girma daga jam'iyyar PDP ta adawa. Tun bayan bulla ta tsohon mataimaki na shugaban kasar Atiku Abubakar a jam'iyyar PDP dai, hankula na masu tsintsiyar ke kara tashi. Kuma sake tabbatar da hadin kai a tsakanin 'yan jam'iyyar ta APC dai a tunani na shugabannin jam'iyyar na zaman hanyar karshe na tabbatar da tasirinsu cikin sabuwar tafiyar mai santsi.