Tafkin Chadi zai sami karin tallafi
September 4, 2018A taron birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus mahalartar taron sun amince cewa za su rubanya sau uku kan irin kudin da suka cimma za su kashe don tallafar kasashen na Tafkin Chadi a taron da suka halarta a birnin Oslo a shekarar bara.
A cewar ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas abin da kasashe suka furta bayarwa ya sha gaban abin da suka yi tsammani. Amirka da Jamus da Hukumar Tarayyar Turai su suka ba da tallafi mafi tsoka cikin kudaden da kasashen da suka halarci taron suka ce za su bayar domin kudinsu ya kai Dala miliyan dubu daya. Taron ya kuma nemi hadin kai na kasashe da ke kewayen tafkin don tallafar al'ummar da ke halin kaka na ka yi.
Kasashen da ke kewayen na Tafkin Chadi dai sun kasance Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya kuma kimanin mutane miliyan biyu da dubu dari uku ne suka kaurace wa muhallansu, sannan sama da miliyan goma sun dogara ne kan kayan tallafi da ake kai wa yankin kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Jamus ta bayyana.
Najeriya dai da aka zarga da rashin tabuka komai wajen ba da nata tallafi ta ce a a ba haka lamarin yake ba don tana aiyuka da suka shafi tsaro da gine-gine na muhallai da asibitoci ga al'ummar yankin na Tafkin Chadi.