Yamai: Taron Hukumar Hana Fasa Kwabri
November 27, 2024Makasudin wannan taron dai shi ne nazarin hanyoyin karfafa hulda tsakanin hukumomin hana fasa kwabri na kasashen yankunan biyu, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani musamman na Internet da kuma hada karfi da karfe wajen tunkarar kalubalan da aikin nasu ke fuskanta musamman masu nasaba da aikata muggan laifuka da suka hadar da ta'addanci da ke barazana ga kokarin da suke na bunkasa tattalin arzikin kasashensu. Jami'an Hukumar Hana Fasa Kwabri da kwararu a fannin zirga-zirgar al'umma da dukiyoyinsu ta kasa da kasa da shugabannin kungiyoyin 'yan kasuwa da na masu fito kimanin 100 ne, daga kasashen Afirka ta Yamma da kuma Afirka ta Tsakiya ke halartar wannan taro.
Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Duniya ce dai ta shirya taron ta shirya a birnin Yamai da nufin hada karfi da karfe wajen gudanar da tsarin aiki na bai-daya da kalubalantar jerin matsalolin da suke fuskanta. Batun yaki da ta'addanci da sauran masu aikata muggan laifuka na kasa da kasa, na daga cikin muhimman batutuwan da wannan taron zai mayar da hankali a kai. Shugabannin kungiyoyin manyan 'yan kasuwa da dama ne suka halarci bikin bude wanan taro, wanda za a kwashe kwanaki uku ana gudanar wa. A karshen taron dai, za a fitar da jerin shawarwari da kuma gyaran wasu tsare-tsare da hukumomin hana fasa kwabri na kasashen Afirkan suka bijiro da su wajen inganta aikinsu da mu'amalarsu, ta yadda za su fi taimaka wa wajen samar wa kasashensu kudin shiga da bunkasa tattalin arzikinsu.