1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Dakile fasa kwabrin makamai

Uwais Abubakar Idris LMJ
September 28, 2023

Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Najeriya ta bayyana sababbin matakan dakile matsalar fasa kwabrin makamai da sauran miyagun kayayyaki ta kan iyakokin kasar, abin da ke kara ta'azzara rashin tsaro da ake fama da shi.

https://p.dw.com/p/4Wvc1
Najeriya | Fasakwabri | Kan Iyaka | Hukumar Hana Fasa Kwabri | Kananan Makamai
Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Najeriya, za ta dakile fasa kwabrin makamai a kan iyakokiHoto: Reuters/J. Penney

Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Najeriyar dai ta dauki wannan matakin ne, kasancewar matsalar fasa kwabrin miyagun kayayyaki na kara bayyana a fili ganin yadda ake ci gaba samun wadanda ke shiga hannun hukuma yayin da suke kokarin shiga da makamai da sauran miyagun kayayyaki ta kan iyakokin Najeriyar. Duk da cewa akwai jami'an tsaro a baki dayan kan iyakokin Najeriyar 114, sai dai har yanzu ana samun wannan matsala. Najeriyar dai ta zama wacce tafi daukan hankali ga masu fataucin makamai da miyagun kwayoyi a wannan yanki na Afirka, ta yiwu saboda karfin tattalin arzikinta da yawan al'ummarta.

Najeriya | Matsala | Makamai | Fasakwabri
Yaduwar makamai a Najeriya, daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tsaroHoto: DW/Katrin Gänsler

Hukumar ta ce baya ga amfani da naurori na zamani da suke taimaka mata wajen kama masu wannan mumunan hali, akwai kuma aiki na hadin guiwa da sauran hukumomin tsaro a Najeriyar. Duk wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ke fuskantar sabon kalubale a kan iyakokinta musamman batun janyewar da Faransa ke son yi daga Jamhuriyar Nijar, abin da hukumar ke sa ido tare da jajircewa. Sai dai bayanai kan yawan kananan makamai da ke hanun mutane ba bisa doka ba da suka kai sama da milyan shida, na nuna akwai sauran aiki a gaba sanin kanana makaman da miyagun kwayoyin babbar barazana ce ga yanayin zaman lafiya a Najeriyar.