1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Yunkurin tallafa wa Siriya don daidaita al'amura

Mahmud Yaya Azare AH
January 13, 2025

Kasashen duniya sun hadu a birnin Riyadh na Saudiya da nufin daukar matakan gaggawa na tallafa wa sabuwar gwamnatin Siriya a siyasance da bangaren agaji .

https://p.dw.com/p/4p7rj
Hoto: Fayez Nureldine/AFP/Getty Images

 Taronda ya sami halartar ministocin harkokin wajen kasashe 29 da ke da ruwa da tsaki kan lamuran Siriya, kasar ta Saudiya ta ce ta shirya shi ne don karawa sabuwar gwamnatin ta Siriya halacci da kuma agaza mata.

Ministan wajen Saudiya yarima Faisal bin Farhan ya ce ta hanyar sassauta wa Siriya takunkuman ne kaɗai, ƙasar za ta iya dawowa cikin  hayyacinta.

“Ina jaddada cewa,janye takunkumi ga Siriya,shi ne matashyar ga tunkaren galibin kalubalen da kasar ke fuskanta. Kamar yadda hakan zai bai wa sabuwar gwamati damar tsayuwa da kafafunta da iya hidimtawa wadanda take mulka.”

Saudi-Arabien Riad 2025 | Syrien-Konferenz | Treffen Außenminister im erweiterten Aqaba-Format
Hoto: Thomas Koehler/AA/IMAGO

An dai yi amanar cewa,masarautar ta Saudiya,mafi karfin tattalin arziki a Gabas ta Tsakiya, na kokarin karfafa karfin faɗa ajinta ne a kasar ta Siriya a yayin da tasirin Iran ke dusashewa a kasar.

A nasa bangaren, sakataren  MDD Antonio Gutteress,ya nemi mahallata taron da su saka wa sadaukar da kan da al,ummar Siriya suka nuna na tsawon shekaru,a fafutukarsu ta sama wa kansu 'yanci da makoma ta gari,ta hanyar tallafa wa sabuwar gwamnatin kasar tsayuwa da kafafuwanta da magance matsalolin agaji da na tattalin arzikin da kasar ke fuskanta:

Saudi-Arabien Riad 2025 | Syrien-Konferenz | Außenminister bin Farhan empfängt syrischen Amtskollegen Al-Shaibani
Hoto: Fayez Nureldine/AFP/Getty Images

‘Ina kira ga duk wadanda ke da ruwa da tsaki kan lamuran Siriya su tashi haikan don tabbatar da dunkulewar kasar karkashin amintaccen jagoranci guda a matakin farko,lamarin da na yi amanar cewa idan har a tabbata,zai magance galibin matsalolin da kasar ke fuskanta.”

Saudi-Arabien Riad 2025 | Syrien-Konferenz | Treffen Außenminister im erweiterten Aqaba-Format
Hoto: Thomas Koehler/AA/IMAGO

Tuni dai kasashen Jamus da Faransada Italiya da Birtaniya suka nuna aniyarsu ta sassauta takunkumin da aka kakaba wa Siriya da ma daukar matakan dageshi, idan har sabuwar gwamnatin ta cika alkawarin da ta dauka wa duniya na yin gaskiya da adalci a mulkin kasar.