1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G7 zai tattauna rikicin Isra'ila da Hamas

Binta Aliyu Zurmi
November 7, 2023

Ministocin harkokin waje na kasashen G7 sun sauka a birnin Tokyo na kasar Japan domin tattaunawa, inda batun rikicin Isra'ila da Hamas zai mamaye taron nasu na kwanaki biyu.

https://p.dw.com/p/4YUtG
Deutschland Münster | Flaggen G7
Hoto: Wolfgang Rattay/AFP/Getty Images

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sauran takwarorinsa na Japan da Faransa da Burtaniya da Jamus da Canada da Italiya za su fidda matsaya guda a kan rikicin a yayin da suke cigaba da shan matsin lamba na neman su saka baki a Isra'ila ta tsagaita wuta.

Faransa ce kadai daga cikin mambobin G7 ta bi bayan Majalisar Dinkin Duniya da ta amince da a gaggauta tsagaita wuta, yayin da Amurka ta bijire, sauran kasashen Jamus da Italiya da Japan da Burtaniya da Canada suka kaurace.

A jiya Litinin bayan ganawarsa da mahukuntan Turkiyya, Blinken ya ce Amurka na kokarin ganin agajin gagawa ya isa ga al'ummar da ke Zirin Gaza.

Tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da harin ramuwar gayya biyo bayan harin ranar 7 na watan Oktoba da ya hallaka Isra'ilawa 1400, dakarun Isra'ila na cigaba da luguden wuta ba kakkautawa a Gaza wanda ya zuwa yanzu ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce sama da mutum 10,000 ne suka rasa rayukansu kuma mafi akasarinsu mata ne da kananan yara.