1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tasirin zaben Brandenburg a siyasar tarayyar Jamus

Abdullahi Tanko Bala MAB
September 23, 2024

Jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ta samu nasara a kan Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a zaben majalisar dokokin jihar Brandenburg. Sai dai akwai ayar tambaya a game da dorewar gwamnatin kawance.

https://p.dw.com/p/4kypy
Da alama, gwamnan Brandenburg Dietmar Woidke ya samu kwanciyar hankali
Da alama, gwamnan Brandenburg Dietmar Woidke ya samu kwanciyar hankaliHoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Brandenburg na daya daga cikin jihohi 16 na tarayyar Jamus. Sannan zaben na jihar ta gabashin Jamus na da matukar tasiri a siyasar kasar baki daya. A cikin makonni uku, jamiyyar AfD mai akidar kyamar baki ta yi kokarin samun angizo idan aka kwatanta da yawan kuri'un da ta samu. Amma mataimakiyar shugaban jamiyyar Green Ricarda Lang ta ce idan har Jam'iyyar da ke take tsarin dimukuradiyya za ta samu Irin wannan sakamakon, ana iya cewa wannan rana ce da 'yan dimukuradiyya ba za su yi murna da ita ba saboda jam'iyyar AfD ta zo a matsayi na biyu a zabe.

Lang ta kara da cewa: "Wannan kalubale ne gare mu baki daya, yadda za mu tinkari wannan, ya kamata mu nuna yadda dimukuradiyya za ta inganta rayuwar al'umma"

Jam'iyyun Greens da FDP sun sha kaye a zaben

Annalena Baerbock a lokacin da ta tabbatar cewar jam'iyyarta Greens ta sha kaye
Annalena Baerbock a lokacin da ta tabbatar cewar jam'iyyarta Greens ta sha kayeHoto: Frank Hammerschmidt/dpa/picture alliance

Ga jam'iyyar rajin kare muhalli ta Greens da kuma jam'iyyar FDP mai sassaucin ra”ayin ci-gaban kasuwanci tare ma da jam'iyyar SPD da suka kafa kawancen gwamnatin tarayya, sun sha ka shi Karo na uku kenan yanzu a jere. Jam'iyyun biyu FDP da Greens sun kasa samun kashi biyar cikin dari na kuri'un da aka kada, wanda shi ne ka'idar samun shiga majalisar dokokin ko wace jiha a Jamus.

Karin bayani:AfD na zawarcin matasa gabanin zabe a Jamus

Sai dai ga Jam'iyyar AfD mai kyamar baki na kallon lamarin ta wata fuska daban, kamar yadda mataimakiyar shugabar Jam'iyyar Alice Weidel ta nunar inda ta nuna gamsuwa tana mai cewa: "Muna farin ciki da sakamakon, ko da yake akwai wasu kuri'iu bisa wasu dalilai na masu kada kuri'a da suka tafi ga Mr. Woidke na SPD. Amma dole ne a amince cewar a wannan fage na siyasa, muna da karfi a gabashin Jamus, mun kuma kasance masu iko kai tsaye a jihohin Saxony da Thuringia. Za mu ga yadda lamura za su kasance a Thuringia."

Jam'iyyar FDP ta yi gargadi kan makomarta

Sakataren FDP Bijan Djir-Sarai na tunani kan makomar jam'iyyar a gwamnatin Jamus
Sakataren FDP Bijan Djir-Sarai na tunani kan makomar jam'iyyar a gwamnatin JamusHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Sakataren Jam'iyyar FDP Bijan Djir-Sarai ya fusata kwarai a jawabin da ya yi bayan da aka bayyana sakamakon zaben Brandenburg. Sai dai Jam'iyyar mai rajin ci-gaban kasuwanci ta dora alhakin mummunan sakamakon a kan kawancen gwamnati a Berlinda a yanzu ya shiga tangal-tangal. Bijan Djir-Sarai  na FDP ya yi bayani da cewa: "Wannan lokaci ne mawuyaci, amma za mu duba gaba da idon basira nan da yan kwanaki. Za mu yi cikakken nazari na halin siyasar da aka shiga a kwamitocinmu na FDP kuma za mu fitar da matsaya"

Karin bayani:Zaben jihohi a Jamus: Nasara ga AfD, hasara ga gwamnati

Shi ma shugaban jam'iyyar SPD Lars Klingbeil ya yi kira da a yanke shawara, amma akwai ayar tambaya ko 'yan siyasar biyu suna nufin abu guda. Klingbeil na magana ne kan ayyukan da kawancen gwamnatin ke son aiwatarwa a zahiri nan da 'yan makonni masu zuwa, misali kan batutuwan fansho, kasafin kudi ko ba da mafakar siyasa. Ya ce: "Muna da gagarumin aiki da za mu yi cikin ‘yan makonni masu zuwa. Muna bukatar yin nasara a saboda haka za mu yi aiki tukuru".

Kujerar shugaban gwamnati a 2025: Merz ko Scholz?

Dan takara na CDU Merz da na SPD Scholz a kujerar shugaban gwamnatin Jamus a 2025
Dan takara na CDU Merz da na SPD Scholz a kujerar shugaban gwamnatin Jamus a 2025Hoto: Florian Gaertner/photothek/picture alliance

Abin mamaki shi ne yadda jam'iyyun CDU da CSU suka bayyana dan takararsu na shugaban gwamnatin tarayya kwanaki kadan kafin zaben Jihar Brandenburg inda suka sanar da sunan Friedrich Merz. A baya dai, Jam'iyyar CDU ta kara rawar gani a zabukan jihohi. Sai dai da ba a bayyana sunanshi ba, tabbas da sai an sake tattaunawa game da cancantarsa a matsayin dan takarar shugaban gwamnati.

Karin bayani:Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka

Ga bangaren mulki, bayan kusan shekaru uku a karagar mulki na kawancen SPD da Greens da  FDP, mutum daya a cikin biyar ke farin ciki da yadda take tafiyar da al'amura musamman kan manyan batutuwa kamar tattalin arziki da ke kwan-gaba kwan-baya da batun 'yan gudun hijira .