1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiTurai

Tattalin arzikin Faransa na bunkasa

Suleiman Babayo AMA
December 17, 2024

Tattalin arzikin Faransa zai ci gaba da bunkasa duk da rikicin siyasar da kasar ke ciki bayan an gaza amincewa da kasafin kudi.

https://p.dw.com/p/4oHEQ
Paris 2024 | Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na kasar FaransaHoto: Ludovic Marin/REUTERS

Tattalin arziki Faransa da ke cikin mawuyacin hali zai smau bunkasa na kaso 0.2 cikin 100 a farkon shekara mai zuwa ta 2025, duk da matsalolin takun saka na siyasa da kasar ta samu kanta game da amincewa da kasafin kudin shekarar badi.

Karin Bayani: Faransa ta yi sabon Firanminista

Hukumar kula da kididdiga ta kasar ta bayyana haka a wannan Talata. Ita dai Faransa tana cikin rudanin siyasa inda majalisar dokoki ta kada kuri'ar yankar kauna ga firaministan kasar game da rikicin kasafin kudi.