1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Najeriya na cikin rudu

Mansur Bala Bello / LMJAugust 25, 2016

Faduwar darajar Naira da kuma kara shiga halin tabarbarewa da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da yi, ya sanya al'ummar kasar cikin halin tasku.

https://p.dw.com/p/1Jpm1
Darajar Naira da tattalin arzikin Najeriya na kara tabarbarewa
Darajar Naira da tattalin arzikin Najeriya na kara tabarbarewaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A Najeriya masana da manazarta na nuna damuwa kan halin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke ci gaba da fadawa. Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa darajar kudin kasar ta Naira na kara karyewa ta yanda ta fadi kasa wanwar. Cikin wannan makon dai an ruwaito cewa darajar Nairar ta yi faduwar da ba a taba gani ba a shekarun baya-bayan nan. Koda cikin wannan mako dai sai da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II wanada kuma ya kasance tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar na CBN, ya nuna damuwarsa kan halin da tattalin arzikin Najeriyar ke sake shiga. 'Yan kasuwa na kokawa kan yadda suke sayen dalar Amirka da tsada duk kuwa da m,atakan da baban bankin Najeriyar na CBN ya ce yana dauka domin saukaka musu, yayin da a hannu guda talakawan kasar ke cikin halin tasku dangane da hau-hawar farashin kayan masarufi a kasar. A baya dai Najeriyar ta kasance kan gaba a fannin tattalin arziki a Nahiyar Afirka, inda ta ke re Afirka ta Kudu, sai dai abin ba haka yake ba a yanzu, domin kuwa tuni tattalin arzikin Najeriyar ya shiga cikin halin ni 'yasu.