1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a tsakanin Iran da Najeriya

February 10, 2011

Iran ta ce ba ta saɓawa takunkumin Majalisar Ɗinkin Duniya ba wajen safarar makamai zuwa Gambiya

https://p.dw.com/p/10Eu7
Shugaban Iran Ahmadinejad yana yiwa babban zauren MDD jawabi(23.09. 2008)Hoto: AP

Jakadan ƙasar Iran a Nijeriya Husseini Abdullah ya bayyana cewar, wani jirgin ruwa ɗauke da makamai dake hanyar sa ta zuwa ƙasar Gambia da Nijeriya ta cafke a tashar ruwan birnin Legas kimanin watanni ukun da suka gabata, bai karya wani takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanyawa ƙasar ba. Jakadan ya ce dalilin sa na faɗin haka shi ne Gambia da Iran sun sanya hannu akan yarjejeniyar da ta shafi makaman ne cikin sirri kimanin shekaru biyu gabannin takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya na haramta safarar makamai daga ƙasar ta Iran zuwa ƙetare.

A cikin shekara ta 2007 ne dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ƙudurin haramta sayan makamai daga Iran, kana ta tsaurara takunkumin a shekara ta 2010. Jakada Husseini Abdullah, ya ce tuni wasu jiragen ruwa biyu ɗauke da makamai daga Iran suka yi nasarar isa ƙasar ta Gambia ta hanyar tashar jiragen ruwan Nijeriya ba tare da wata matsala ba. Nijeriya dai ta gurfanar da wani ba-Iraniye a gaban kotu, kuma wasu ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya na binciken kayayyakin da jirgin ke ɗauke da su.

Mawallafi . Saleh Umar Saleh

Edita : Usman Shehu Usman