1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tiani ya gode wa 'yan Nijar da suka ba da tallafi

Salissou Boukari MAB
October 12, 2023

Yayin da takunkumin da ECOWAS da UEMOA suka kakaba wa Nijar ke kawo cikas ga fannin tattalin arziki, 'yan kasar da ke kasashen waje sun kai tallafin kudade ga hukumomin soja domin gudanar da mahimman ayyuka raya kasa.

https://p.dw.com/p/4XSR7
	
Shugaban mulkin sojan Nijar Abdourahamane Tiani
Shugaban mulkin sojan Nijar Abdourahamane TianiHoto: Télé Sahel/AFP

Wasu 'yan kasar Nijar da ke birnin Lome na kasar Togo da kuma wadanda ke birnin Dubai na Haddadiyar Daular Larabawa sun mika wa hukumomin mulkin sojan kasarsu kudade har miliyan 110 na CFA a matsayin gudunmawarsu ga kokowar da kasar ke yi ta neman cikakken 'yanci. Adamou Mamane Batoure da ke zama jami'i a ofishin jakadancin  Nijar a Togo ya kawo wannan kudi da kanshi zuwa ga hukumomin na Nijar. Ya ce: "Kasarmu na fama da matsaloli sabili da takunkumi, abin da ya sa ('yan Nijar matzauna Togo) suka tattara miliyan 100 na CFA domin a kawo ma hukumar CNSP tare da ba su cikakken goyon baya.

Karin bayani: Jadawalin zaben 'yan Nijar mazauna ketare

Miliyan 110 na CFA ne 'yan Nijar mazauna ketare suka kai wa gwamnatin mulkin soja
Miliyan 110 na CFA ne 'yan Nijar mazauna ketare suka kai wa gwamnatin mulkin sojaHoto: SEYLLOU/AFP

A bangarensu, 'yan kasar Nijar da ke da zama a birnin Dubai sun kawo miliyan 10 na CFA ga kasarsu. Abdoulrazak Mahamane da ke wakiltar 'yan Nijar da ke Dubai da ya kawo wadannan kudade ya ce: " Mun raba kudin gida biyu: kashi daya a saka a baytalmani na hukumar CNSP, kashi na biyu kuma a mika shi a hannun shugaban kwamitin farar hula da ke kokoaar neman cikakken 'yanci a dandalin juriya na Escadrille.”

A cikin kasar ta Nijar ma, al'ummar garin Koulli Koira da ke cikin yankin jihar Tillabery sun tattara kudade 300,000 na CFA da suka danka a hannun hukumomin mulkin soja. Tuni ma hukumomin Yamai suka sanar da bude wurin ajiye wadannan kudade a cikin banki domin bai wa 'yan kasar damar zubawa kai tsaye ga duk wanda yake son tallafawa.

Karin bayani:Nijar na tankiya da Faransa

Janar Tiani ya yi godiya ga 'yan kasar Nijar tare da kiransu ga hadin kai
Janar Tiani ya yi godiya ga 'yan kasar Nijar tare da kiransu ga hadin kaiHoto: REUTERS

Wannan ne ya sanya shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi amfani da dama domin isar da godiya ga 'yan kasar ta Nijar da ke tallafa wa gwamnati. Sai dai cikin jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta Nijar, shugaban ya ce ya kamata su kasance masu hadin kai a duk inda suke, sannan masu neman ganin an kama wannan ko wancan su yi hakuri domin aiki ne shari'a, kuma shari'a za ta yi aikinta ba tare da wani tsambare ba. 

Kungiyoyin da ke fafutika sun nuna gamsuwarsu da wannan tallafi na 'yan Nijar mazauna ketare.