1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jadawalin zaben 'yan Nijar mazauna ketare

Gazali Abdou Tasawa
May 30, 2022

A wani yunkuri na zaben cike gurbi na majalisar dokoki, hukumar zaben Nijar ta fitar da jadawalin rijistar sunayen masu kada kuri'a daga kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/4C3Y4
Niger Wahlen Unabhängige Wahlkommission (CENI)
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A Jamhuriyar Nijar, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, ta fitar da jadawalin aikin rijistar masu zabe na kasashen ketare a wani mataki na shirin gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisar dokoki biyar a tsakanin 'yan kasar ta Nijar mazauna kasashen ketare wanda kundin tsarin mulkin kasar ne ya tanada. Annobar Corona ce dai ta yi dalilin kasa gudanar da zaben ‘yan Nijar mazauna kasashen ketare a lokacin da kasar ta shirya zaben gama gari wanda aka shirya a ranar 21 ga watan feburairun 2021.

Niger Agadez Afrika
Shirin gudanar da zaben 'yan Nijar mazauna kasashen wajeHoto: Getty Images/Afp/Boureima Hama

Kundin tsarin mulkin Nijar ya tanadi kujeru 171 ne a majalisar dokokin kasar. Sai dai A zaben gama gari na shugaban kasa zagaye na farko da aka yi a jumulce da na 'yan majalisar dokoki a kasar  a ranar 27 ga watan Disamba 2021 da ya gabata, annobar Corona ba ta bai wa hukumar ta CENI damar iya shirya zaben ba na 'yan Nijar mazauna ketare, wanda ya sa a halin yanzu majalisar ke kunshe da 'yan majalisa 166.

A kan haka ne a yanzu bayan kura ta fara lufawa, hukumar zaben kasar ta Nijar ta dukufa aikin shirya zaben cike gurbin na kujeru biyar na 'yan majalisar dokoki a tsakanin 'yan Nijar mazauna ketare. Inda a yanzu take shirin farawa da yin aikin rijistar 'yan nijar mazauna ketare. 

Daga cikin kasashe goma sha biyar da Nijar ta tsaida domin shirya zaben a cikinsu, takwas na Kungiyar ECOWAS ne da suka hada da Najeriya da Cote d’ivoire da Burkina Faso da Mali da Senegal da Togo da kuma Benin da Ghana. Sai kuma biyu a Afirka ta Tsakiya da suka hada da Chadi da Kamaru, sai Maroko da Aljeriya daga yankin Maghreb, sai kasashen EU da suka hada da Faransa da Beljiyam daga Turai sai kuma Amirka.

Hukumar zaben ta yi kira ga 'yan Nijar mazauna wadannan kasashe da su kwana cikin shiri. A karshen makon da ya gabata, hukumar zaben ta gana da 'yan siyasa da kuma 'yan farar hula domin gabatar masu da aikin nata.