Shugaba Tinubu ya bayyana takainsa a kan sace dalibai
March 8, 2024Talla
A cikin wata sanarwar fadar gwamnatin kasar Tinibu ya ce ya samu bayanai daga Jami'an tsaro,kan satar guda biyu, wanda ya ce ya bayar da umurni da a gaggauta cetosu. Sannan ya janjanta wa iyalan wadanda abin ya shafa yana mai ba su tabbacin cewar nan ba da dadewa ba za su sake haduwa da 'yan uwansu. A cikin wannan mako ne dai aka sace wasu mata kusan dari biyu a Jihar Borno, yayin da aka sake kame wasu daliban sama da dari biyu a Kaduna.