Tirka tirka a tattara sakamakon zaben Bayelsa
November 13, 2023Tun a ranar lahadi ne dai jami'an zabe suka fara aikin karbar bayanan kuriun da a ka kada daga kananan hukumomi takwas da ke jihar ta Bayelsa. An dai ta samun tsaikon wannan aiki, a dalilai da wahalar isowar jamian zabe daga sassan kananan hukumomin bakin ruwa wato Riverine Communities,da kuma takaddama kan sakamakon zaben wasu kananan hukumomi biyu da ake zargi an yi aringizon kuriu da ya dara adadin ma su rajistar zabe, gami ma da zanga zanga da a ka yi ta yi a daura da hedikwatar hukumar zabe ta Jahar, kan zargin almundahana.
Mr Wilfred Ifoga, wani jamiin hukumar zabe da ke Bayelsa ya yi karin haske.
"Ya ce tuni aka kammala aikin kananan hukumomi shida, kuma a ragowar biyun da ake dako, daya na gab da kammaluwa.
Kafin fara aikin tattara alkaluman zaben ragowar kananan hukumomin biyu dai, wato Brass da Ijaw ta kudu,a hukumance, PDP na da kuriu 137,909 APC na da 73,503.
A na dai sa ran kammala tattara alkaluman zaben na Bayelsa a wannan ranar ta Litinin tare da sanar da wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan.
A can kuwa jihar Imo da tuni hukumar INEC ta sanar da Hope Uzodinma na jamiyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, bukukuwa kawai magoya baya ke yi, yayin da jamiyyun Labor da PDP ke ci gaba da watsi da sakamakon. Wasu 'yan jihar ta Imo da suke tsokaci sun baiyana bukatar sojoji da 'yan sanda su daina katsalandan a harkokin zabe, wanda suka ce ta haka ne za a gane masu hana ruwa gudu.