Traore zai samar wa Burkina faso tashar makamashin nukiliya
October 13, 2023Talla
Wannan ci-gaban ya samu ne a daidai lokacin da ake gudanar da taron makon makamashi na kasar Rasha a birnin Moscow, wanda ministan makamashin Burkina Faso Simon-Pierre Boussim ya halarta. Burkina Faso na shigo da kaso mai tsoka na wutar lantarkinta daga makwabtanta Côte d' Ivoire da Ghana.
Karin bayani:Taron kasashe kan inganta amfani da nukiliya a duniya
Amma za ta kasance kasa ta biyu ta nahiyar Afirka da za ta mallakin tashar makamashin nukiliya, baya ga wacce Afirka ta Kudu ta malkaka a Koeberg da ke kusa da Cape Town. Dama dai Burkina Faso da ke yankin Sahel da kuma ke karkashin mulkin soja tun shekarar da ta gabata na neman fadada abokan huldarta ciki har da Rasha don samun ci-gaban rayuwa.