Ko Trump ya kama hanyar komawa White House?
January 16, 2024Mr. Trump ya doke tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley da gwamnan jihar Florida Ron DeSantis, lamarin da ya kai shi matakin kusa da tabbatar da mafarkinsa a zaben shugaban kasa karo na uku a jere.
Sai dai a Talatar ake sa ran Trump zai gurfana a gaban kotu a birnin New York, inda ake tuhumarsa da laifuka 91 da suka shafi yunkurin murde sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2020.
Yadda sakamakon zaben ya kasance a Iowa
Bayan da aka kirga kusan dukkan kuri’un, Trump ya samu kashi 51 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda ya doke Gwamnan Florida Ron DeSantis da kashi 21 cikin 100 na kuri'un, ya kuma ba da rata maai yawa ga tsohuwar Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley wacce ta samu kashi 19 cikin 100.
Karin bayani:Trump ya daukaka kara zuwa kotun koli
Don haka a sauƙaƙe Trump ya zarce yawan kuri'un da Bob Dole ya samu a 1988 na kashi 12.8 cikin 100 a jam'iyyar Republican a jihar Iowa.
Sakamakon da jihar ta samu ya tabbatar da sakamakon zaben kasar da ya nuna Trump, mai shekaru 77, yana kan gaba a fafatawar da ta yi na zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican.
Dan kasuwa Vivek Ramaswamy, wanda shi ma yana daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar Republican, a halin yanzu ya zama dan kallo bayan da ya samu kuri’u kasa da kashi 8 cikin 100 a Iowa, inda ya amince da Trump a wani jawabi da ya yi wa magoya bayansa bayyana sakamakon.
karin bayani:Trump bai halarci mahawarar 'yan takarar jam'iyyarsa ba
An dai samu karancin fitowar masu kada kuri’a cikin shekaru 25, maiyuwa ne sakamakon yanayin sanyi da hadarin mota da ke barazana ga rayuwa a jihar.
A yanzu dai 'yan takarar sun nufi jihar New Hampshire da ke arewa maso gabashin kasar, inda za a gudanar da zabuka na biyu nan da kwanaki takwas.
Wane martani ake yi ga sakamakon?
"Na gode IOWA, INA SON ku duka!!!" Trump ya rubuta a cikin manyan haruffa a dandalin sa na sada zumunta na Truth Social, biyo bayan labarin nasarar da ya samu.
A jawabin da ya yi na samun nasara, Trump ya bukaci hadin kan kasa. Inda yace "A gaskiya ina ganin wannan lokaci ne yanzu da kowa da kowa, kasar, za su hadu wuri guda," in ji shi.
"Da alama Donald Trump ya ci nasara a Iowa. Shi ne fitaccen dan takara a daya bangaren a wannan lokacin" a cewar Shugaba Joe Biden, wanda zai fafata da Trump a watan Nuwamba 2024 idan ya tabbata Trump ya samu nasafrar zama dan takara a jam'iyyar Republican.