Najeriya: Tsadar hasken wutar lantarki
May 13, 2024'Ya'yan kungiyar kodagon Najeriyar sun kuma toshe ma'aikatar kula da samar da wutan lantarki ta Najeriyar da ke Abujar, domin nuna adawarsu da karin kudin hasken wutar lantarkin da aka yi wa wani sashi na masu amfani da ita a kasar. Dubban ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da ke karkashin kungiyoyin kodagon Najeriyar ne, suka yi dafifi a shalkwatar samar da hasken wutan lantarki ta Najeriya suna dauke da kwalaye da aka rubuta kalaman da ke nuna adawar tasu. Shugabannin kungiyar kodagon dai sun dage kan cewa ba za ta sabu ba, kan wannan kari da aka yi wa mutanenen da ke samun hasken wutar lantarkin da ya kai sao'i 20 a kowace rana. Gwamnatin Najeriyar dai ta yi karin kudin hasken wutar lantarkin ne ga rukunin da suka bayyana na daya daga Naira 66 kowane kilowatt ya zuwa Naira 225, karin da yake shi ne mafi yawa da aka yi a kasar.
Kungiyar kodagon dai ba kawai tana zanga-zanga a kan karin kudin ba ne, tana ma son a duba daukacin yadda aka sayar da hakar samar da hasken wutar lantakin da aka mayar da ita hannun 'yan kasuwa. 'Ya'yan kungiyar kodogon ta Najeriya dai, sun kai ga yin barazana ta afkawa ma'aikatar samar da wutar lantarkin Najeriyar, muddin babu jami'in gwamnatin da ya fito ya saurare su. Wannan dai zanga-zanga ce da aka yi a dukkanin jihohin Najeriyar 36, domin yin matsin lambar da kungiyar kodagon ke fatan zai sanya a biya bukatarsu kamar yadda suka matsawa gwamnatin ta janye harajin laifuffukan da ake aikatawa ta Internet bayan adawar da aka yi da shi. Ba dai wannan karon ne kungiyar kodogon ta Najeriya ta fara shirya irin wannan zanga-zangar ba, domin kuwa ta sha shirya irinta a lokuta da dama.