Tsadar takardun kudaden waje a Najeriya
February 1, 2024Daukacin masu hada-hadar canjin kudaden kasashen waje a Abuja hedikwatar Najeriya ne suka dauki wannan mataki na rufe kasuwar ruf, domin nuna damuwarsu a kan ci gaba da tsadar da takardar kudi ta dallar Amurka ke yi, wacce ita ce mizani na auna farashin sauran kudaden da ake hada–hada da su.
Kasuwa dai a kan ce a kai maki dole. A bisa tsari na tattalin arziki dai farashin kaya na dogara ne ga bukatarsa da kuma yawan wanda aka samar, abin da ke sanya ya ragu ko ya karu. Wannan ya sanya a lokutan baya gwamnati kan shiga kasuwar ta samar da dalar domin rage farashinta, abin da ta dakatar domin barin kasuwa ta yi halinta. Amma rufe kasuwar zai iya taimaka maido da darajar takardun kudi na Naira ta Najeriyar da ta sha kashi.
Tuni dai aka shiga kame-kame a kokari na ceto darajar takardun kudin Najeriyar ta Naira, inda babban bankin kasar ya bai wa daukacin bakuna umurni su fito da dalar da suka adana su sayar wa masu bukata.
A yayin da kasuwar ‘yan canjin da ke Abuja take a rufe bayanai na nuna akwai masu hada-hadar ta bayan fage domin abu ne mai wahala a hana duk wani dan canji hada-hadar kudadden kasashen waje musamman a tsarin da ake da ba shi da cikakken tsarin tabbatar da hana hada-hada a kasuwar da take a rufe.